Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 19:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 19:9
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”


Allah na Isra'ila ya yi magana, Matsaron Isra'ila ya ce mini, ‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci, Wanda yake mulki da tsoron Allah,


Wata rana za a yi wani sarki mai adalci, da kuma shugabannin ƙasa waɗanda za su yi mulki da gaskiya.


Yehoshafat kuma ya naɗa waɗansu Lawiyawa, da firistoci, da waɗansu shugabannin iyalan Isra'ilawa, saboda su yi shari'a tsakani da Ubangiji, su daidaita tsakanin masu jayayya. A Urushalima za su zauna.


A duk lokacin da 'yan'uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari'a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari'a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da 'yan'uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi.


Idon Ubangiji fa, yana kai da komowa ko'ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya. Ka yi wauta a cikin wannan al'amari. Tun daga yanzu har zuwa nan gaba za ka yi ta fama da yaƙoƙi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ