2 Tarihi 19:10 - Littafi Mai Tsarki10 A duk lokacin da 'yan'uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari'a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari'a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da 'yan'uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |