2 Tarihi 18:31 - Littafi Mai Tsarki31 Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, suka ce, “Wannan ne Sarkin Isra'ila,” sai suka juya suka yi yaƙi da shi. Amma Yehoshafat ya yi kururuwa, Ubangiji Allah ya kuɓutar da shi, Allah kuwa ya kawar da su daga gare shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202031 Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙi suka ga Yehoshafat, sai suka yi tsammani, “Wannan ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juya don su yaƙe shi, amma Yehoshafat ya yi ihu, Ubangiji kuma ya taimake shi. Allah ya janye su daga gare shi, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”