Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 18:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji abin da Allahna ya faɗa mini, shi zan faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji, zan faɗa masa kawai abin da Allahna ya faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 18:13
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa ya ce wa Bal'amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal'amu ya tafi tare da dattawan Balak.


Na ce, ‘Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Ubangiji ba, in aikata nagarta ko mugunta bisa ga nufin kaina.’ Abin da Ubangiji ya faɗa shi ne zan faɗa.”


sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu, ya damƙa mana amanar bishara, haka muke sanar da ita, ba domin mu faranta wa mutane rai ba, sai dai domin mu faranta wa Allah, shi da yake jarraba zukatanmu.


To, wato ni son mutane nake nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya? Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.


Domin mu ba kamar mutane da yawa muke ba, masu yi wa Maganar Allah algus, mu kaifi ɗaya ne, kamar yadda Allah ya umarce mu, haka muke magana a gaban Allah, muna na Almasihu.


Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki gurasa,


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.


Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu'a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”


Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.


Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”


Bal'amu kuwa ya amsa wa Balak, ya ce, “Ban faɗa maka ba, duk abin da Ubangiji ya faɗa, shi ne zan yi?”


Bal'amu kuwa ya ce, “Ai, ba tilas ne in hurta abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”


Jarumin fa da ya je ya kira Mikaiya ɗin, ya ce masa, “Ka kula fa, dukan maganganun da annabawa suke yi, sun yi wa sarki daɗi. Don haka kai ma ka yi maganar da za ta gamshi sarki kamar yadda suka yi.”


Da Mikaiya ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu haura zuwa Ramot-gileyad mu fāɗa mata da yaƙi, ko in haƙura?” Mikaiya kuwa ya amsa, ya ce, “Ka haura, gama za ka ci nasara, gama za a bashe su a hannunka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ