2 Tarihi 17:9 - Littafi Mai Tsarki9 Suka koyar a Yahuza, suna tare da Littafin Shari'ar Ubangiji, wato Attaura. Suka shiga ko'ina a biranen Yahuza suka koyar da jama'a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Suka yi koyarwa a dukan Yahuda, suna ɗauke da Littafin Dokar Ubangiji tare da su; suka tafi ko’ina a dukan garuruwan Yahuda suka koyar da mutane. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra'ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama'arsa Isra'ila.