Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 17:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Mai biye da Yehohanan kuma shi ne shugaba Amasiya, ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa don bauta wa Ubangiji, shi kuma yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000) gwarzaye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 biye da shi, Amasiya ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa da yardar rai don hidimar Ubangiji, yana da sojoji 200,000.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 17:16
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra'ila, Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Sai jama'a suka yi murna da ganin yadda suka bayar hannu sake, gama sun kawo sadakokinsu a gaban Ubangiji da zuciya ɗaya, shi sarki Dawuda kuma ya yi murna ƙwarai.


Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Isra'ilawa suka ƙudura su yi yaƙi. Mutane suka sa kansu da farin ciki. Alhamdu lillahi!


Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.


A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.


Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama'arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.


“Amma wane ni ko kuma jama'ata, da za mu iya kawo sadaka mai yawa haka? Gama dukan kome daga gare ka yake. Daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.


Mai bi masa, sai shugaba Yehohanan yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000).


Na Biliyaminu kuma sarkin yaƙi shi ne Eliyada, gwarzo ne, yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000), 'yan baka da garkuwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ