Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 16:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Idon Ubangiji fa, yana kai da komowa ko'ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya. Ka yi wauta a cikin wannan al'amari. Tun daga yanzu har zuwa nan gaba za ka yi ta fama da yaƙoƙi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 16:9
38 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci, Yana kuma sauraron roƙonsu. Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”


Ubangiji yana ganin abin da yake faruwa a ko'ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta.


Gama ina ganin dukan ayyukansu, ba a ɓoye suke a gare ni ba, muguntarsu kuma ba a ɓoye take a gare ni ba.


Ubangiji yana ganin dukan abin da kake yi. Inda ka shiga duk yana kallonka.


Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,


“Gama yana ganin al'amuran mutum, Yana kuma ganin dukan manufarsa.


Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.


Gama wane ne ya taɓa raina ranar ƙananan abubuwa? Amma za su yi murna da ganin igiyar awo a hannun Zarubabel. Waɗannan fitilu bakwai su ne alama Ubangiji yana kai da kawowa a duniya.”


Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan 'yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa.


Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu'ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,


Amma ya duba ƙasa, Ya dubi sammai da duniya.


Dubi mutumin kirki, ka lura da adali, Mutumin salama yakan sami zuriya,


Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ɗauke hankalinku? Ku da aka bayyana muku Yesu Almasihu gicciyeyye sosai.


Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’


Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai saboda abin nan da na aikata. Amma ina roƙonka ka gafarta mini laifina, gama na yi aikin wauta ƙwarai da gaske.”


“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.


Sama'ila kuwa ya ce wa Saul, “Ka yi wauta, ba ka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba. Dā Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra'ila har abada.


Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba'asha Sarkin Isra'ila dukan kwanakin sarautarsu.


Kai, marar azanci! Abin da ka shuka, ai, ba zai tsiro ba sai ya mutu.


Amma ba a kawar da masujadan da yake Isra'ila ba, duk da haka zuciyar Asa sarai take, ba wani aibi duk kwanakinsa.


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


‘Ku ji wannan, ya ku wawaye, marasa hankali, Kuna da idanu, amma ba ku gani, Kuna da kunnuwa, amma ba ku ji.’ ”


Bayan da Dawuda ya ƙidaya mutane, sai lamirinsa ya kā da shi, ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka gafarta mini, gama na yi wauta.”


Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama'a.


Allah ya san dukan abin da nake yi, Yana ƙididdige dukan takawata.


Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi.


“Ku bi titunan Urushalima ko'ina! Ku dudduba ku lura! Ku bincika kowane dandali, ku gani, Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya Mai aikata adalci, mai son gaskiya, Sai in gafarta mata.


Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.


Don me ba ka bari na sumbaci 'ya'yana mata da maza na yi bankwana da su ba? Kai! Ka yi aikin wauta.


Ba a kuma ƙara yin wani yaƙi ba har shekara ta talatin da biyar ta mulkinsa Asa.


Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma.


Amma ikon Allah yana kan dattawan Yahudawa, saboda haka ba su hana su yin ginin ba, sai sun kai wa Dariyus labari, sun sami amsa a rubuce tukuna.


Saboda yana ganin duniya ɗungum, Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.


Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya.


Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa, Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.


Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ