5 Da Ba'asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi.
5 Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.
Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha, Sarkin Isra'ila a dukan kwanakin mulkinsu.
Ben-hadad kuwa ya kasa kunne ga sarki Asa, ya aika da shugabannin rundunan sojojinsa suka yi yaƙi da biranen Isra'ila. Suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan biranen ajiya na Naftali.
Sa'an nan sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuza, suka kwashe duwatsun da katakan da Ba'asha yake gina Rama da su, ya gina Geba da Mizfa da su.
Da Ba'asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.