2 Tarihi 16:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sa'an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Sai Asa ya ɗauki azurfa da zinariya daga ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma na fadansa ya aika wa Ben-Hadad sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa'an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.