2 Tarihi 15:9 - Littafi Mai Tsarki9 Sai ya tattara dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, da kuma na Ifraimu, da na Manassa, da na Saminu, waɗanda suke zaman baƙunci tare da su. Da yawa daga cikin Isra'ilawa suka yi ƙaura zuwa wurinsa, sa'ad da suka ga Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Sa’an nan ya tattara dukan Yahuda da Benyamin da kuma mutane daga Efraim, Manasse da Simeyon waɗanda suke zaune a cikinsu, gama jama’a mai girma ta zo wurinsa daga Isra’ila sa’ad da suka ga cewa Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.