Sai Ruhun Allah ya sauko wa Zakariya, ɗan Yehoyada, firist, ya tsaya a gaban jama'a ya yi magana da su, ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Don me kuke ƙetare umarnan Ubangiji, har da za ku rasa albarka? Saboda kun rabu da bin Ubangiji, shi ma ya rabu da ku.’ ”
Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi.
Akwai mutum biyu da suka ragu a zangon, sunan ɗayan Eldad, ɗayan kuwa Medad. Ruhun kuma ya zauna a kansu gama suna cikin dattawan nan da aka lasafta, amma ba su fita zuwa alfarwa ba, sai suka yi annabci a zangon.