2 Tarihi 14:7 - Littafi Mai Tsarki7 Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa.