2 Tarihi 14:14 - Littafi Mai Tsarki14 Suka hallaka dukan birane da suke kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka washe dukan biranen, gama biranen suna cike da ganima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Suka hallaka dukan ƙauyukan kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka kwashi ganima na dukan ƙauyukan nan, da yake akwai ganima sosai a can. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.