Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 13:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 13:8
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”


Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.


Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”


Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu.


Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba, Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.


Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”


ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.


Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra'ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.”


Amma ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka riga ka, ka yi wa kanka gumaka, da siffofi na zubi, ka tsokane ni in yi fushi, ka yi watsi da ni.


Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ