Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 13:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Abaija ya tafi da rundunar jarumawansa, dubu ɗari huɗu (400,000) zaɓaɓɓun mutane. Yerobowam shi kuma ya jā dāgar yaƙi don ya kara da Abaija, yana da mutum dubu ɗari takwas (800,000), zaɓaɓɓun mayaƙa ƙarfafa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Abiya ya tafi yaƙi tare da mayaƙa dubu ɗari huɗu jarumawa, Yerobowam kuwa ya ja dāgār yaƙi a kan Abiya da mayaƙa dubu ɗari takwas jarumawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 13:3
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama'ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra'ila, su komo wa Rehobowam da mulki.


Yowab ya kawo wa Dawuda adadin yawan mutanen. Jimillar dukan Isra'ila zambar dubu ne da dubu ɗari (1,100,000) waɗanda za su iya yaƙi. Jimillar mutanen Yahuza kuwa dubu ɗari huɗu da dubu saba'in ne (470,000) waɗanda suka isa zuwa yaƙi.


Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.


Ya yi mulki shekara uku a Urushalima, sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Uriyel na Gibeya. Sai yaƙi ya ɓarke a tsakanin Abaija da Yerobowam.


Sai Abaija ya hau kan Dutsen Zemarayim, wanda yake a ƙasar Ifraimu mai tuddai, ya ce, “Ku kasa kunne gare ni, ya Yerobowam da dukanku Isra'ilawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ