Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 13:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Abaija ya runtumi Yerobowam, ya ƙwace masa waɗansu birane, wato Betel tare da ƙauyukanta, da Yeshana tare da ƙauyukanta, da kuma Efron tare da ƙauyukanta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 13:19
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa'an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.


Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim.


Saboda haka, Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da take a bakin jeji, ya shiga wani gari, mai suna Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran.


Sa'ad da Isra'ilawan da suke a wancan hayi na kwarin da waɗanda suke a wancan hayin Urdun suka ga mayaƙan Isra'ila sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar garuruwansu, suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.


Joshuwa kuma ya ci dukan biranen sarakunan nan, da dukan sarakunansu. Ya kashe su da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.


Ya cinye ta da yaƙi, da sarkinta, da garuruwanta. Ya buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Kamar yadda ya yi wa Hebron, da Libna da sarkinta, haka kuma ya yi wa Debir da sarkinta.


Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a hannunku.”


Haka kuwa aka ci nasara a kan mutanen Isra'ila a wannan lokaci. Mutanen Yahuza sun yi rinjaye saboda sun dogara ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.


Mulkin Yerobowam bai ƙara farfaɗowa a zamanin Abaija ba. Ubangiji kuma ya bugi Yerobowam, ya mutu.


Ya kira sunan wurin nan Betel, amma da farko, sunan birnin, Luz.


Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ