2 Tarihi 12:7 - Littafi Mai Tsarki7 Da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai ya yi magana da Shemaiya cewa, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Sa’ad da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai wannan maganar Ubangiji ta zo wa Shemahiya, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ku tafi ku yi tambaya a wurin Ubangiji domina, da kuma domin sauran waɗanda suka ragu a Isra'ila da Yahuza, a kan abin da littafin da aka gāno ya faɗa, gama Ubangiji ya yi fushi da mu da hasala mai tsanani saboda kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji, su aikata bisa ga dukan abin da aka faɗa a wannan littafi ba.”