Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 12:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Aka faɗo masa da karusai dubu da ɗari biyu (1,200), da mahayan dawakai mutum dubu sittin (60,000). Mutanen da suka taho tare da sarki Shishak daga Masar, ba a san adadinsu ba, akwai Libiyawa, da Sukkimiyawa, da kuma Habashawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Da kekunan yaƙi dubu ɗaya da ɗari biyu da kuma mahayan dawakai dubu haɗe da mayaƙan Libiyawa, Sukkatawa da kuma Kushawa waɗanda suka wuce ƙidaya suka zo tare da shi daga Masar,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 12:3
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Habasha da Masar su ne ƙarfinta marar iyaka, Fut da Libiya su ne kuma mataimakanta.


Ai, Habashawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da karusai da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, sai ya bashe su a hannunka.


Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tamani na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Habasha da yaƙi.


Yawan rundunonin sojan doki kuwa, na ji adadinsu zambar dubu metan ne.


“Yaƙi zai ci Habasha, da Fut, da Lud, da dukan Arabiya, da Libya, da mutanen ƙasar da suka haɗa kai da su.”


Gama ni ne Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, wanda ya cece ku. Zan ba da Masar, da Habasha, da Seba Ga Sairus domin fansarku.


Ubangiji kuwa ya fatattaki Habashawa a gaban Asa da Yahuza, Habashawa kuwa suka gudu.


Sai Zera mutumin Habasha ya zo da soja zambar dubu (1,000,000) da karusa ɗari uku har Maresha, don ya yi yaƙi da su.


Amma Suriyawa suka gudu daga gaban Isra'ilawa. Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa, mahayan karusai ɗari bakwai, da mahayan dawakai dubu arba'in (40,000). Aka yi wa Shobak shugaban rundunarsu rauni wanda ya zama ajalinsa, a can ya rasu.


Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000), da mahayan dawakai dubu shida (6,000), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen.


Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar.


Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al'ummai, har zuwa Kogin Kishon.


gama Ubangiji ya sa sojojin Suriyawa suka ji amon karusai, da na dawakai, da na babbar rundunar soja. Sai suka ce wa junansu, “Ai, Sarkin Isra'ila, ya yi ijara da sarakunan Hittiyawa, da na Masarawa, su zo su fāɗa mana.”


Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ