Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.
Ba a ɓoye na yi magana ba, Ban kuwa ɓoye nufina ba. Ban ce jama'ar Isra'ila Su neme ni a kowace hanyar ruɗami ba. Ni ne Ubangiji, gaskiya kuwa nake faɗa, Ina sanar da abin da yake daidai.”
Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, daga kowace kabilar Isra'ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.
Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kakanninmu, ka tabbatar da yardar rai ɗin nan a rayukan jama'arka, ka bi da zukatansu zuwa gare ka.
Sa'an nan Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”