Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa'an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa,
Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.
Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta.
sa'ad da sojojin Sarkin Babila suke yaƙi da Urushalima da kuma dukan biranen da suka ragu na Yahuza, wato Lakish da Azeka. Waɗannan su kaɗai ne biranen Yahuza masu garu da suka ragu.
Daga lokacin da Amaziya ya bar bin Ubangiji, sai suka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, amma ya gudu zuwa Lakish, sai suka sa a bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.