Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.
Sai Eliyezer ɗan Dodawahu mutumin Maresha, ya yi annabci gāba da Yehoshafat, ya ce, “Saboda ka haɗa kanka da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Don haka jiragen ruwa suka farfashe, suka kāsa tafiya Tarshish.
Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.