Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa.
Filistiyawa kuma sun kai hari a biranen ƙasar Shefela, da Negeb ta Yahuza, har suka ci Bet-shemesh, da Ayalon, da Gederot, da Soko da ƙauyukanta, da Timna da ƙauyukanta, da Gimzo da ƙauyukanta. Sai suka zauna a can.