Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
“Ya ku mutanen Biliyaminu, ku gudu neman mafaka, Daga cikin Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa, Ku ba da alama a Bet-akkerem, Gama masifa da babbar halaka sun fito daga arewa.
Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa'ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”
Sun kuwa zauna a waɗansu wurare guda biyar, wato Itam, da Ayin, da Rimmon, da Token, da Ashan, da ƙauyukan da suke kewaye, har zuwa kudu maso gabas da garin Ba'al: Ga lissafin iyalansu da wuraren da suka zauna.
sai ya aika zuwa Tekowa a kira masa wata mace mai hikima. Da ta zo, ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki, ki sa rigunan makoki, kada ki shafa mai. Ki yi kamar wadda ta yi kwanaki da yawa tana makokin rasuwar wani.