Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Dawuda ya riga ya haura da akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim zuwa inda ya shirya dominsa, domin yă kafa masa tenti a Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 1:4
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suka ajiye shi a wurinsa a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa dominsa. Dawuda ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama a gaban Ubangiji.


Sai ya tafi tare da su duka zuwa Kiriyat-yeyarim domin ya kawo akwatin Alkawarin Allah, wanda ake kira da sunan Ubangiji Mai Runduna wanda yake zaune a tsakanin kerubobin.


Suka fa shigo da akwatin alkawarin Allah, suka ajiye shi a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa masa, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama a gaban Allah.


Dawuda kuwa ya gina wa kansa gidaje a birninsa, ya kuma kafa alfarwa domin akwatin alkawari na Allah.


Sai Isra'ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim.


Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.


Yanzu kuwa na gina maka ƙasaitaccen ɗaki, Na gina maka wurin da za ka zauna har abada.”


Saboda haka Dawuda ya tattara Isra'ilawa duka a Urushalima don a kawo akwatin alkawarin Ubangiji a wurinsa, inda aka riga aka shirya masa.


ya ce musu, “Ku ne shugabanni na gidajen kakanninku, Lawiyawa. Sai ku tsarkake kanku da 'yan'uwanku domin ku iya kawo akwatin alkawarin Allah na Isra'ila a inda na shirya masa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ