Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai Sulemanu ya tara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), sai ya sa su a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai, ya kasance da kekunan yaƙi dubu da ɗari huɗu da kuma dawakai dubu goma sha biyu, waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, da kuma tare da shi a Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 1:14
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba'in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000).


Sulemanu kuwa yana da ɗakunan dawakai da na karusai dubu huɗu (4,000), yana da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000) waɗanda suke zaune a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da sarki.


da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.


Sarki Sulemanu ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu da zinariya. Anyi kowace garkuwa da shekel ɗari shida na zinariya.


Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’


Saboda haka sai ka sa a saro mini itatuwan al'ul na Lebanon. Barorina za su haɗu da barorinka, ni kuwa zan biya ka aikin da barorinka za su yi bisa ga yadda ka ce, gama ka sani ba wani daga cikin mutanena da ya iya saran katako kamar mutanenka.”


da kuma Ba'alat da dukan biranen ajiya waɗanda yake da su, da birane don karusansa, da birane don mahayan dawakansa, ya gina dukan abin da yake bukata a Urushalima, da Lebanon, da a dukan ƙasashen da suke cikin mulkinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ