Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 9:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Amma da suka tafi don su binne ta, ba su tarar da kome ba sai ƙwaƙwalwa, da ƙafafu, da tafin hannuwanta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Amma sa’ad da suka je don su binne ta, ba su sami kome ba sai ƙoƙon kanta, ƙafafunta da kuma hannuwanta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 9:35
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Nan take sai mala'ikan Ubangiji ya buge shi don bai ɗaukaka Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.


Saboda haka Ubangiji ya ce Yehoyakim, Sarkin Yahuza, ba zai sami magāji wanda zai zauna a gadon sarautar Dawuda ba. Za a jefar da gawarsa a waje ta sha zafin rana, da dare kuma za ta sha matsanancin sanyi.


Za a binne shi kamar jaki, Za a ja shi a yar a bayan ƙofofin Urushalima.”


Mai yiwuwa ne mutum ya haifi 'ya'ya ɗari ya kuma yi tsawon rai, amma kome tsawon ransa ba wani abu ba ne idan ba shi da farin ciki, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba. Sai na ce, gara jaririn da aka haifa matacce da shi.


Yakan aika da masifa da lalacewa Ga waɗanda suke aikata abin da ba daidai ba.


Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel, ba wanda zai binne ta.” Sa'an nan ya buɗe ƙofar, ya gudu.


Sa'an nan Yehu ya shiga gida, ya ci ya sha, ya ce, “Ku san yadda za ku yi da wannan la'ananniyar mace, ku binne ta, gama ita 'yar sarki ce.”


Sai suka komo, suka faɗa masa. Sai ya ce musu, “Wannan, ai, faɗar Ubangiji, wadda ya faɗa ta bakin bawansa Iliya Batishbe, ya ce, ‘Karnuka za su cinye naman Yezebel a cikin Yezreyel.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ