Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 9:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Fādawansa suka ɗauke shi a cikin karusar zuwa Urushalima, suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Barorinsa suka ɗauke shi cikin keken yaƙi zuwa Urushalima suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 9:28
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Barorinsa kuwa suka ɗauke shi daga cikin karusa, suka sa shi a karusa ta biyu, suka kawo shi Urushalima, sai ya rasu. Aka binne shi a hurumin kakanninsa. Yahuza da Urushalima fa suka yi makoki domin Yosiya.


Fādawansa kuwa suka ɗauko gawarsa a karusa daga Magiddo, suka kawo Urushalima, suka binne a kabarinsa. Sai jama'ar ƙasa suka naɗa Yehowahaz ɗan Yosiya sarki a matsayin tsohonsa.


Sai suka kawo shi a bisa dawakai, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda.


Ya kuma karkashe dukan firistocin matsafai na kan tuddai a bisa bagadan da suke can. Ya ƙone ƙasusuwansu a bisa bagadan. Sa'an nan ya komo Urushalima.


Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.


Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa'ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.” Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.


Sa'an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.


Yoram kuwa ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Ahaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ