Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 9:26 - Littafi Mai Tsarki

26 ‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 ‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin ’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 9:26
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Za ku yi tambaya cewa, ‘Me ya sa ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba?’ Sa'ad da ɗan ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, ya kiyaye dokokina sosai, lalle zai rayu.


Amma bai karkashe 'ya'yansu ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Shari'a, wato Attaura ta Musa, inda Ubangiji ya yi umarni cewa, “Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, ba za a kuma kashe 'ya'ya saboda iyaye ba, amma mutum zai mutu saboda laifin kansa.”


Sa'ad da suka tafi, sun bar shi da rauni mai tsanani ƙwarai, sai barorinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a gadonsa, saboda ya kashe ɗan Yehoyada firist. Ya mutu, aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba su binne shi a kabarin sarakuna ba.


Ka faɗa masa, ni Ubangiji, na ce, ‘Ka kashe mutum, kana kuma ƙwace abin da ya mallaka?’ Ka faɗa masa ga abin da na faɗa, ‘A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka.’ ”


“Kada a kashe ubanni maimakon 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata.


Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Sai suka fitar da shi daga cikin birni, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.


Yehoram kuwa ya ce, “Ku shirya karusa.” Suka shirya masa karusa. Sa'an nan Yehoram Sarkin Isra'ila, da Ahaziya Sarkin Yahuza suka fita, kowa a cikin karusarsa, suka tafi su taryi Yehu. Suka sadu da shi a daidai gonar Nabot mutumin Yezreyel.


Yehu ya ce wa Bidkar, “Ka ɗauke shi ka jefar a gonar Nabot mutumin Yezreyel, gama ka tuna sa'ad da ni da kai muke kan dawakai muna biye da Ahab, tsohonsa, yadda Ubangiji ya faɗi wannan magana a kansa cewa,


Ka jawo wa gidanka kunya, Saboda ka karkashe mutane da yawa, Ka hallaka kanka da kanka.


Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai! Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini! Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ