2 Sarakuna 8:4 - Littafi Mai Tsarki4 A lokacin kuwa sarki yana tare da Gehazi, wato baran annabi Elisha, ya ce, “Ka faɗa mini dukan mu'ujizan da Elisha ya yi.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Sarki kuwa yana magana da Gehazi bawan mutumin Allah, ya ce masa, “Ba ni labarin dukan abubuwan banmamakin da Elisha ya yi.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.”