Yehoram Sarkin Isra'ila ya tafi tare da Sarkin Yahuza da Sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.
Sai Sarkin Mowab ya kama babban ɗansa, wanda zai gāji sarautarsa, ya miƙa shi hadayar ƙonawa a kan garu. Isra'ilawa kuwa suka tsorata ko allahn abokan gāba zai cuce su, don haka suka janye, suka koma ƙasarsu.