Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 8:16 - Littafi Mai Tsarki

16 A shekara ta biyar ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 8:16
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ahaziya kuwa ya mutu bisa ga maganar Ubangiji, daidai yadda Iliya ya faɗa. Sai ɗan'uwansa Yehoram ya gāji gadon sarautarsa a shekara ta biyu ta Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, gama Ahaziya ba shi da ɗa.


A shekara ta goma sha takwas ta sarautar Yehoshafat Sarkin Yahuza, Yehoram ɗan Ahab ya zama Sarkin Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha biyu.


Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.


Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara ashirin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Azuba 'yar Shilhi.


Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.


A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.


Amma Yehosheba 'yar sarki Yoram, 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba.


Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan 'yan'uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ