Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 8:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 8:1
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na kawo fari a kan ƙasa, da kan tuddai, da kan hatsi, da kan 'ya'yan inabi, da kan 'ya'yan zaitun, da kan dukan abin da yake tsirowa daga ƙasa, da kan mutane, da kan dabbobi, da kan ayyukansu.”


Sa'ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu, Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,


A zamanin da mahukunta suke mulkin Isra'ila, aka yi yunwa a ƙasar. Sai wani mutumin Baitalami a Yahudiya ya yi ƙaura zuwa ƙasar Mowab, shi da matarsa, da 'ya'yansa maza biyu.


Da yaron ya yi girma, sai wata rana ya bi mahaifinsa gona zuwa wurin masu girbi.


A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.


Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra'ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa'ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar.


Sai Iliya ya tafi. A lokacin kuwa yunwa ta tsananta a Samariya.


Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”


Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.


Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabas, ya miƙe tsaye, ya yi faɗi da ikon Ruhu, cewa za a yi wata babbar yunwa, a duniya duka, an yi ta kuwa a zamanin Kalaudiyas.


Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.


Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al'amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama.


Gama ga shi, na fara sa masifa ta yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana. To, kuna tsammani ba za a hukunta ku ba? Sai an hukunta ku, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’


Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani, Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.


Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kuwa kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gabanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu sai ka yi tunani, ka faɗi irin amsar da zan mayar wa Ubangiji da ya aiko ni.”


A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.”


Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”


Maimaitawar mafarkin nan na Fir'auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al'amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.


Yusufu ya ce wa Fir'auna, “Mafarkin Fir'auna ɗaya ne, Allah ya bayyana wa Fir'auna abin da yake shirin aikatawa.


Aka sāke yin yunwa a ƙasar, banda wadda aka yi a zamanin Ibrahim. Sai Ishaku ya tafi Gerar wurin Abimelek, Sarkin Filistiyawa.


aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci.


Elisha kuwa ya koma Gilgal sa'ad da ake fama da yunwa a ƙasar. Sa'ad da ƙungiyar annabawa suke zaune a gabansa, sai ya ce wa baransa, “Dora babbar tukunya, ka dafa wa annabawan nan fate-fate.”


Haka kuwa ya zama gama mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu.


Sai matar ta tashi, ta yi kamar yadda annabi Elisha ya faɗa mata. Ta tafi, ita da iyalinta suka zauna a ƙasar Filistiyawa har shekara bakwai.


Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.”


Ubangiji ya ce, “Ai, ni ne, na sa a yi yunwa a biranenku. Shi ya sa ba ku da abinci. Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ