2 Sarakuna 7:4 - Littafi Mai Tsarki4 Idan mun ce, ‘Bari mu shiga birni,’ yunwa tana birnin, za mu mutu a wurin. Idan kuma mun zauna a nan za mu mutu. Saboda haka bari mu tafi sansanin Suriyawa, idan sun bar mu da rai, za mu rayu, idan kuwa sun kashe mu, za mu mutu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 In muka ce, ‘Za mu shiga cikin birni’ yunwa tana can, za mu kuwa mutu. Idan kuwa muka zauna a nan, za mu mutu. Saboda haka, bari mu ƙetare zuwa sansanin Arameyawa mu miƙa kai. Idan suka bar mu da rai, to; idan kuwa suka kashe mu, shi ke nan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.