Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa'ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”
Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra'ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama'ar nan a ƙasar da na ba su ba.”
Dogarin ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji da kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu zai yiwu ke nan?” Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka amma ba za ka ci ba.”
Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.”
Amma sa'ad da bawana ya yi annabci, Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena, Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika. Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can, Za a kuma sāke gina biranen Yahuza. Waɗannan birane za su daina zama kufai.