Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”
Sai sarki ya tashi da dare ya ce wa fādawansa, “Bari in faɗa muku irin shirin da Suriyawa suka yi a kanmu. Sun sani muna fama da yunwa, domin haka suka fita daga sansanin suka ɓuya a karkara, suna nufin sa'ad da muka fita daga birnin, sai su kama mu da rai, sa'an nan su shiga birnin.”