7 Sa'an nan ya ce, “Ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu, ya ɗauka.
7 Sai ya ce masa, “Ka ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu ya ɗauka.
Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.”
Sai ta koma ta faɗa wa annabi Elisha, shi kuwa ya ce mata, “Ki je ki sayar da man, ki biya bashin, abin da ya ragu kuwa ki ci, ke da 'ya'yanki.”
Ya kuwa miƙa mata hannu ya tashe ta. Sai ya kira tsarkaka da matan waɗanda mazansu suka mutu ya miƙa musu ita rayayyiya.
Mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuwa ya ba da shi ga uwa tasa.
Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka ka kama wutsiyarsa.” Ya miƙa hannunsa ya kama shi, ya zama sanda kuma a hannunsa.
Sa'an nan Elisha ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?” Da ya nuna masa wurin, sai ya karyi tsumagiya, ya jefa a wurin, ya sa ruwan gatarin ya taso bisa kan ruwan.
Wata rana, sa'ad da Sarkin Suriya yake yaƙi da Isra'ila, sai ya shawarci fādawansa, suka zaɓi wurin da za su kafa sansani.