misali, idan mutum ya tafi jeji, shi da abokinsa don su saro itace. Da ya ɗaga gatari don ya sari itace, sai ruwan gatarin ya kwaɓe daga ƙotar, ya sari abokinsa har ya mutu. Irin wannan mai kisankai zai gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen don ya tsira,
Amma sa'ad da ɗaya daga cikinsu yake saran wani gungume, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe ya fāɗa a ruwa. Sai ya yi ihu, ya ce, “Wayyo, maigida, me zan yi? Abin aro ne.”