Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 6:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Ya ce, “Allah ya yi mini hukunci mai tsanani, idan ban fille kan Elisha ɗan Shafat yau ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani har ma fiye da haka, idan ban cire kan Elisha ɗan Shafat yau ba!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 6:31
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”


Inda za ki rasu, ni ma can zan rasu, a binne ni. Idan na bar wani abu ya raba ni da ke, in dai ba mutuwa ba, to, Ubangiji ya yi mini hukunci mai zafi!”


Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama'a, da duk jama'a ta halaka.”


Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”


Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”


Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne, wanda kake wahalar da Isra'ila?”


Sai sarki Sulemanu ya rantse da Ubangiji ya ce, “Allah ya kashe ni nan take idan ban sa Adonija ya biya wannan roƙo da ransa ba.


Ku ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”


Mutane kuwa suka zo su ba Dawuda magana, ko ya ci abinci tun rana ba ta faɗi ba. Amma Dawuda ya rantse ya ce, “Allah ya buge ni in mutu nan, idan na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi.”


Allah ya la'anta ni, idan ban yi wa Dawuda abin da Ubangiji ya rantse masa ba,


Allah ya buge ni in mutu, idan na bar masa wani mutum da rai kafin gobe da safe.”


Sai Saul ya ce, “Allah ya yi mini abin da ya fi haka, idan ba a kashe ka ba, Jonatan.”


Eli ya tambaye shi, ya ce, “Me Ubangiji ya faɗa maka? Kada ka ɓoye mini. Allah zai hukunta ka idan ka ɓoye mini abin da ya faɗa maka.”


Ben-hadad kuwa ya sāke aikawa wurinsa ya ce, “Bari alloli su kashe ni idan ban kai mutane da yawa da za su hallaka Samariya ba.”


sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na'aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.”


Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ