Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 6:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Da baran annabi Elisha ya tashi da sassafe, ya fita waje, sai ga sojoji, da dawakai, da karusai sun kewaye gari. Sai baran ya ce, “Wayyo, maigidana! Me za mu yi?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Sa’ad da bawan mutumin Allah ya farka ya kuma fita kashegari da sassafe, sai ga mayaƙa tare da dawakai da kekunan yaƙi sun kewaye birni. Sai bawan ya ce, “Ranka yă daɗe! Me za mu yi?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 6:15
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!


Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”


Amma sa'an nan za su firgita ƙwarai, Irin yadda ba su taɓa yi ba, Gama Allah ya warwatsa ƙasusuwan maƙiyanka. Ya kore su sarai, saboda ya ƙi su.


Sai Musa ya tashi, shi da baransa Joshuwa, suka tafi, suka hau dutsen Allah.


Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami'un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu.


Amma sa'ad da ɗaya daga cikinsu yake saran wani gungume, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe ya fāɗa a ruwa. Sai ya yi ihu, ya ce, “Wayyo, maigida, me zan yi? Abin aro ne.”


Saboda haka kuturtar Na'aman za ta kama ka, kai da zuriyarka har abada.” Haka kuwa ya fita a wurinsa kuturu, fari fat kamar auduga.


sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na'aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.”


Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji ne a nan, wanda zai tambayar mana Ubangiji?” Sai ɗaya daga cikin fādawan Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, na'ibin Iliya.”


Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.


Sai ya aika da dawakai, da karusai, da sojoji da yawa. Suka tafi da dare suka kewaye garin.


Elisha kuwa ya ce masa, “Kada ka ji tsoro gama waɗanda suke tare da mu, sun fi waɗanda suke tare da su yawa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ