Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Amma sa'ad da Elisha, annabin Allah, ya ji cewa Sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya aika wa sarki ya ce, “Me ya sa ka keta tufafinka? Bari ya zo wurina, zai sani akwai annabi a Isra'ila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Da Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra’ila ya yayyage tufafinsa, sai ya aika masa da wannan saƙo, “Don me za ka yayyage tufafinka? Ka sa mutumin yă zo wurina, zai kuwa san cewa akwai annabi a Isra’ila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:8
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da ku al'ummai fa nake. Tun da yake ni manzo ne ga al'ummai, ina taƙama da aikina,


Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra'ila daga Masar, Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.


Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.


Ya kuwa komo wurin annabi Elisha shi da jama'arsa duka, ya zo ya tsaya a gabansa, ya ce, “Yanzu na sani a duniya duka ba wani Allah banda na Isra'ila, saboda haka, sai ka karɓi kyauta daga wurina.”


Da Sarkin Isra'ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”


Wata rana sai ta ce wa uwargijyarta, “Da a ce ubangijina yana tare da annabin nan wanda yake Samariya, da ya warkar da shi daga kuturtarsa!”


Suka ce masa, “Wani mutum ya sadu da mu, ya ce mana, mu koma wurinka mu shaida maka, ‘Ubangiji ya ce, ba Allah a Isra'ila, har aka aike ku ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron? Domin haka ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”


Sai macen ta ce wa Iliya, “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuwa yana magana ta wurinka.”


Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara.


Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace.


Amma baran ya ce masa, “Ai, akwai wani mutumin Allah a garin nan, ana kuwa ganin girmansa, domin duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa, watakila ya iya faɗa mana inda jakunanmu suke.”


Amma Ubangiji Allah ya yi magana da annabi Shemaiya,


Na'aman kuwa da dawakansa da karusansa suka tafi suka tsaya a ƙofar gidan Elisha.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ