Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Da Sarkin Isra'ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Da sarkin Isra’ila ya karanta wasiƙar, sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne? Zan iya ɗauke rai ko in mai da shi? Me ya sa wannan mutum ya turo mini wannan mutum in warkar da kuturtarsa? Dubi fa yadda yake nemana da faɗa!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:7
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar, Yana kai mutane kabari, Ya kuma tā da su.


Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da 'ya'yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”


Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”


“ ‘Ku duba fa, ni ne shi, Ba wani Allah, banda ni, Nakan kashe, in rayar, Nakan sa rauni, nakan kuma warkar, Ba wanda zai cece su daga hannuna.


suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.


Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji, Gama shi ne ya yayyaga, Shi ne kuma zai warkar. Shi ne ya yi mana rauni, Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.


Abin nan da sarki yake so a yi masa yana da wuya, ba wanda zai iya biya wa sarki wannan bukata, sai dai ko alloli waɗanda ba su zama tare da 'yan adam.”


Amma da manzannin nan, Barnaba da Bulus, suka ji haka, suka kyakketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ɗaga murya suna cewa,


Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!


Duk da haka da sarkin da barorinsa suka ji maganar, ba wanda ya ji tsoro, balle su keta rigunansu don baƙin ciki.


Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.


Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”


Da suna da hikima, da sun gane wannan, Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!


Sai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu.


Sa'ad da Ra'ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa,


Ya kai wa Sarkin Isra'ila tarkardar, wadda ta ce, “Sa'ad da wannan takarda ta sadu da kai, ka sani fa, ni ne na aiko barana, Na'aman, wurinka domin ka warkar da shi daga kuturtarsa.”


Amma Yusufu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ni ba a matsayin Allah nake ba.


Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ