Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?” Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Sa’an nan ya shiga ya tsaya a gaban maigidansa Elisha. Sai Elisha ya tambaye shi ya ce, “Ina ka je, Gehazi?” Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Bawanka bai je ko’ina ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:25
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gehazi ya ce, “Lafiya ƙalau, maigidana ne ya aiko ni in faɗa maka, yanzu yanzu waɗansu samari biyu daga ƙungiyar annabawa suka zo wurinsa daga ƙasar tudu ta Ifraimu, yana roƙonka, ka ba ni talanti ɗaya na azurfa da rigunan ado guda biyu in kai masa.”


Suna cikin cin abinci, sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”


Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.


Ga yadda al'amarin mazinaciya yake, takan yi sha'aninta sa'an nan ta yi wanka ta ce, “Ban yi laifin kome ba!”


Sai annabi Ishaya ya tafi wurin sarki Hezekiya ya ce masa, “Daga ina ne waɗannan mutane? Me suka ce maka?” Hezekiya ya amsa, ya ce, “Sun zo daga ƙasa mai nisa, wato Babila.”


Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?” Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”


Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?” Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?”


Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi.


Azariya ya yi fushi, a lokacin kuwa yana riƙe da farantin ƙona turare a hannunsa, sa'ad da ya yi fushi da firistocin, sai kuturta ta faso a goshinsa, a nan gaban firistocin a cikin Haikalin Ubangiji, wajen bagaden ƙona turare.


Kawun Saul kuwa ya tambaye shi, shi da baransa, “Ina ne kuka tafi?” Saul ya ce, “Mun je neman jakuna, da ba mu same su ba, sai muka tafi wurin Sama'ila.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ