Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Na'aman kuwa ya ce, “In ka yarda ka karɓi talanti biyu na azurfa.” Ya ƙirga su ya ɗaure kashi biyu, da kuma rigunan ado masu kyau ya ɗora wa barorinsa biyu, ya umarce su su kai wa Gehazi har gida.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Na’aman ya ce, “Ba damuwa, karɓi talenti biyu.” Ya roƙi Gehazi yă karɓa, sa’an nan ya ƙunsa masa talentin biyu na azurfa ya sa masa a kan jakankuna biyu, ya haɗa da tufafi kashi biyu, ya ba bayinsa biyu suka ɗauka, ya ce su sha gaban Gehazi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:23
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.


Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba.


Sa'ad da suka gani akwai kuɗi da yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki, da babban firist suka zo, suka ƙirga kuɗin da yake a Haikalin Ubangiji suka ƙunsa shi a babbar jaka.


Ɗaya daga cikinsu kuwa ya ce, “In ka yarda, ka tafi tare da mu.” Elisha kuwa ya yarda, ya ce, “To, mu tafi.”


Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.” Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.


Amma suka matsa masa har suka i masa, sai ya yardar musu su tafi. Su kuwa suka tafi su hamsin. Suka yi ta neman Iliya, har kwana uku, amma ba su same shi ba.


Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da 'ya'yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”


Sai Sarkin Suriya ya ce, “Ka tafi yanzu, zan aika wa Sarkin Isra'ila da takarda.” Na'aman kuwa ya ɗauki azurfa na talanti goma, zinariya kuma na shekel dubu shida (6,000), da rigunan ado guda goma, ya kama hanya.


Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ