Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Gehazi ya ce, “Lafiya ƙalau, maigidana ne ya aiko ni in faɗa maka, yanzu yanzu waɗansu samari biyu daga ƙungiyar annabawa suka zo wurinsa daga ƙasar tudu ta Ifraimu, yana roƙonka, ka ba ni talanti ɗaya na azurfa da rigunan ado guda biyu in kai masa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Gehazi ya amsa ya ce, “Lafiya ƙalau. Maigidana ne ya aiko ni cewa, ‘Samari biyu daga ƙungiyar annabawa sun ziyarce ni daga ƙasa mai duwatsu na yankin Efraim. Ina roƙonka ka ba su talenti na azurfa da tufafi kashi biyu.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:22
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Sarkin Suriya ya ce, “Ka tafi yanzu, zan aika wa Sarkin Isra'ila da takarda.” Na'aman kuwa ya ɗauki azurfa na talanti goma, zinariya kuma na shekel dubu shida (6,000), da rigunan ado guda goma, ya kama hanya.


Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”


Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.


Kowane mutum yana ruɗin maƙwabcinsa da abokinsa, Ba mai faɗar gaskiya, Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya. Suna aikata laifi, Sun rafke, sun kasa tuba.


Ubangiji ya ce, “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, Ƙarya ce take rinjayar gaskiya a ƙasar. Suna ta cin gaba da aikata mugunta, Ba su kuwa san ni ba.


Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.


Akwai wata ƙungiyar annabawa da take a Betel suka zo, suka ce wa Elisha, “Ko ka sani, yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?” Elisha ya ce, “I, na sani, amma mu bar zancen tukuna.”


Sa'ad da sarki yake wucewa, sai ya kira sarki, ya ce, “Ni baranka na tafi yaƙi, sai ga shi, soja ya kawo mini mutum, ya ce mini, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi ya kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’


Ubangiji ya umarci wani daga cikin annabawa ya ce wa abokinsa bisa ga umarnin Ubangiji, “Ina roƙonka ka buge ni.” Abokinsa kuwa ya ƙi ya buge shi.


Sa, an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.


Ele'azara, ɗan Haruna kuma ya rasu, aka binne shi a Gebeya a garin ɗansa, Finehas, wanda aka ba shi a ƙasar tuddai ta Ifraimu.


Samson kuwa ya ce musu, “Bari in yi muku ka-cici-ka-cici, idan kun faɗa mini amsarsa a kwana bakwai na bikin, to, zan ba ku rigunan lilin talatin da waɗansu riguna talatin na ado.


Ruga ka tarye ta, ka tambayi lafiyarta, da ta mijinta, da ta ɗanta.” Ta amsa, ta ce, “Lafiya ƙalau.”


Gehazi kuwa ya bi bayan Na'aman. Da Na'aman ya ga wani yana biye da shi a guje, sai ya sauka daga karusarsa, ya juya ya tarye shi, ya ce, “In ce ko lafiya?”


Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?” Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”


Ƙungiyar annabawa da take Yariko suka zo wurin Elisha suka ce masa, “Ko ka sani yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?” Ya ce, “Na sani, amma mu bar zancen tukuna.”


Waɗansu annabawa hamsin kuma suka tafi tare da su. Iliya da Elisha suka tsaya kusa da kogi, annabawa hamsin ɗin suka tsaya da ɗan nisa.


Sa'ad da annabawa hamsin da suke Yariko suka ga ya haye ya nufo su, sai suka ce, “Ai, ruhun Iliya yana kan Elisha.” Sai suka tafi su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ