Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:20 - Littafi Mai Tsarki

20 sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na'aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 sai Gehazi, bawan Elisha mutumin Allah, ya yi tunani a ransa ya ce, “Maigidana ya yi wa Na’aman mutumin Aram nan ƙaramci da bai karɓi duk abin da ya kawo ba. Muddin Ubangiji yana a raye, zan bi shi a guje in karɓi wani abu daga gare shi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:20
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya ce wa baransa, Gehazi, “Kirawo matan nan.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a gabansa.


Ya ce, “Allah ya yi mini hukunci mai tsanani, idan ban fille kan Elisha ɗan Shafat yau ba.”


Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.”


Gehazi kuma ya yi gaba, ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma ba motsi ko alamar rai. Saboda haka ya koma, ya taryi Elisha, ya faɗa masa yaron bai farka ba.


Lalle ne kuwa, kowane mai kula da ikkilisiya, da yake shi mai riƙon amana saboda Allah ne, yă zama marar abin zargi, ba mai taurinkai ba, ko mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai saurin dūka, ko mai kwaɗayin ƙazamar riba.


domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.


“Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.


ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma.


sai ya ɓoye wani abu daga cikin kuɗin, da sanin matarsa, ya kawo sashin kuɗin kurum ya ajiye a gaban manzanni.


Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi.


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.”


Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.


Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.”


da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.


“Tasa ta ƙare, shi wanda ya arzuta gidansa da ƙazamar riba, Ya kuma gina gidansa a bisa don ya tsere wa masifa!


Amma ka sa idonka da zuciyarka ga ƙazamar riba, Da zubar da jinin marar laifi, Da yin zalunci da danniya.


Malalaci yana ganin kansa mai hikima ne fiye da mutum bakwai waɗanda suke da dalilai a kan ra'ayinsu.


Mugun mutum yana fāriya da mugayen manufofinsa, Mai haɗama yakan zagi Ubangiji ya kuma ƙi shi.


Hakika, duk wanda ya yi laifin za a kashe shi, ko da Jonatan ne, ɗana.” Amma ba wanda ya ce kome.


“Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”


Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”


Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.” Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.


Gehazi kuwa ya bi bayan Na'aman. Da Na'aman ya ga wani yana biye da shi a guje, sai ya sauka daga karusarsa, ya juya ya tarye shi, ya ce, “In ce ko lafiya?”


A lokacin kuwa sarki yana tare da Gehazi, wato baran annabi Elisha, ya ce, “Ka faɗa mini dukan mu'ujizan da Elisha ya yi.”


Elisha kuwa ya tafi Dimashƙu. A lokacin kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, yana ciwo. Aka faɗa masa cewa, annabi Elisha ya zo, yana nan,


Elisha kuwa ya husata, ya ce, “Da ma ka caka sau biyar ko shida da za ka yi nasara a kan Suriyawa har ka ci su sarai, amma yanzu za ka yi nasara da su sau uku kawai.”


Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel. Sa'ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can.


Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila, Ku da kuke zuriyar Yahuza. Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji, Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila, Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.


Da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba gajiyayyu!”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ