Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Sai dai Ubangiji ya gafarta mini lokacin da na bi sarki zuwa cikin haikalin Rimmon, gunkin Suriya, don ya yi sujada. Na gaskata Ubangiji zai gafarta mini.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Amma ina fata Ubangiji zai gafarta wa bawanka saboda abu guda. Bari yă gafarta mini sa’ad da na raka sarkina zuwa haikalin Rimmon domin yă yi sujada, bari Ubangiji yă yi wa bawanka gafara saboda wannan.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:18
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.” Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”


Ubangiji ya yi alkawari da 'ya'yan Yakubu, ya kuma umarce su kada su yi wa gumaka sujada ko su durƙusa musu, ko su bauta musu, ko su miƙa musu hadayu.


Sarki kuwa ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa'ad da sarki ya tafi wurinsa.


Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.


Duk da haka zan rage mutum dubu bakwai (7,000) na Isra'ila waɗanda ba su rusuna wa Ba'al da gwiwoyinsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”


domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ