Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 5:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Ashe, kogin Abana da na Farfar, wato kogunan Dimashƙu, ba su fi dukan ruwayen Isra'ila ba? Da ban yi wanka a cikinsu na tsarkaka ba?” Ya juya, ya yi tafiyarsa da fushi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ashe, Amana da Farfa, kogunan da suke Damaskus, ba su fi dukan ruwan da suke Isra’ila ba? Me zai sa ba zan nutse cikinsu in tsarkaka ba?” Sai ya juya ya yi tafiyarsa da fushi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 5:12
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun.


“A ran nan za a buɗe maɓuɓɓuga don wanke zuriyar Dawuda da mazaunan Urushalima daga zunubi da rashin tsarki.


Mutum mai hankali yake danne fushinsa. Lokacin da wani ya cuce ka, abin kirki ne, ka yi kamar ba ka kula da shi ba.


Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ƙi ne.


Na'aman kuwa ya ce, “Da yake ka ƙi ka karɓa, ina roƙonka, ka ba baranka labtun alfadari biyu na ƙasa, gama nan gaba baranka ba zai ƙara miƙa hadaya ta ƙonawa ko baiko ga wani gunki ba, sai dai Ubangiji.


Sai ya ɗauki alkyabban nan da ta faɗo daga wurin Iliya, ya bugi ruwan, yana cewa, “Ina Ubangiji, Allah na Iliya?” Sa'ad da ya bugi ruwan, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, Elisha kuwa ya haye.


Sa'an nan Iliya ya tuɓe alkyabbarsa, ya naɗe ta, ya bugi ruwa da ita, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, dukansu biyu fa suka taka sandararriyar ƙasa suka haye.


A wannan rana ruwa mai rai zai gudano daga Urushalima. Rabinsa zai nufi tekun Gishiri, rabi kuma zai nufi Bahar Rum. Zai riƙa malalowa rani da damuna.


Amma Na'aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni.


Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.


Amaryata, ki taho daga Dutsen Lebanon, Taho daga Lebanon. Ki taho daga ƙwanƙolin Dutsen Amana, Da Dutsen Senir da Harmon, Inda zakuna da damisoshi suke zaune.


Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Dimashƙu, “Hamat da Arfad sun gigice, Domin sun ji mugun labari, sun narke saboda yawan damuwa, Ba za su iya natsuwa ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ