Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 4:43 - Littafi Mai Tsarki

43 amma baran ya ce, “Ƙaka zan raba wa mutum ɗari wannan abinci?” Elisha ya sāke cewa, “Ka ba mutane su ci, gama Ubangiji ya ce za su ci har su bar saura.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 Sai bawansa ya ce, “Yaya zan raba wa mutane ɗari wannan?” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Ka raba wa mutane su ci, gama haka Ubangiji ya ce, ‘Za su ci har su bar saura.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 4:43
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ya ce musu, “Ku ku ba su abinci mana.” Suka ce, “Ai, abin da muke da shi bai fi gurasa biyar da kifi biyu ba, sai dai in za mu je mu sayo wa dukkan jama'an nan abinci ne.”


Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu.


“Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”


Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har aka kwashe ragowar gutsattsarin, kwando goma sha biyu.


“To, gurasa bakwai da na gutsuttsura wa mutum dubu huɗu fa? Manyan kwanduna nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Bakwai.”


Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.


Sai almajiransa suka amsa masa suka ce, “Ina za a iya samun gurasar da za ta ciyar da mutanen nan a jeji haka?”


A ina zan samo nama da zan ba wannan jama'a duka? Gama suna ta gunaguni a gabana, suna cewa, ‘Ba mu nama mu ci.’


Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ