11 Wata rana da Elisha ya zo, ya shiga ɗakin, ya huta.
11 Wata rana da Elisha ya zo, sai ya haura ɗakinsa ya kwanta.
Bari mu gina masa ɗan ɗaki a kan bene, mu sa masa gado, da tebur, da kujera, da fitila, don duk sa'ad da ya zo ya sauka a wurin.”
Sai ya ce wa baransa, Gehazi, “Kirawo matan nan.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a gabansa.
Wata rana Elisha ya wuce zuwa Shunem inda wata mace take da zama, sai ta gayyace shi cin abinci. Don haka duk lokacin da ya bi ta wannan hanya, sai ya ratsa ta gidanta, ya ci abinci.