Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 3:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ya kuma aika wa Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ce, “Sarkin Mowab ya tayar mini, ko za ka yarda ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowabawa?” Yehoshafat ya ce, “Zan tafi, ni kamarka ne, mutanena kuma kamar mutanenka, dawakaina kuma kamar naka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?” Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 3:7
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kuma ce wa Yehoshafat, “Za ka tafi tare da ni zuwa wurin yaƙi a Ramot-gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa Sarkin Isra'ila, “Ni da kai ɗaya ne, mutanena kuma mutanenka ne, dawakaina kuma naka ne.”


Sai Ahab, Sarkin Isra'ila, ya ce wa Yehoshafat, Sarkin Yahuza, “Za ka tafi tare da ni zuwa Ramot-gileyad?” Sai ya amsa, ya ce, “Ni ma kamarka ne, jama'ata kuma kamar jama'arka ce, za mu je yaƙin tare da kai.”


Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka.


Sai sarki Yehoram ya fita daga Samariya a lokacin, ya tattara Isra'ila duka.


Wace hanya za mu bi?” Yehoram kuwa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”


Yehoram Sarkin Isra'ila ya tafi tare da Sarkin Yahuza da Sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.


Elisha kuwa ya rasu, aka binne shi. Maharan Mowabawa sukan kawo yaƙi a ƙasar da bazara.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ